- Kwaɗaitarwa a kan koyan alwala da sunnonita da kuma ladubbanta, kana da aiki da hakan.
- Falalar alwala, kuma tana kankare zunubai ƙanana, amma manya sai an musu tuba.
- Sharaɗin fitar laifukan shi ne cika alwalar, da kuma yinta ba tare da kurakurai ba, kamar dai yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana.
- Kankare zububai a wannan Hadisin an ƙayyadeshi ne da nisantar manyan laifuka, da kuma tuba daga su, Allah maɗaukaki ya ce: Idan kuka nisanci manyan abubuwan da ake hanaku, to, zamu kankare muku laifukanku.