- Muhimmancin sanar da yara al'amuran addini na tauhidi da ladubba da sauransu.
- Sakamako yana kasancewa daga irin aikin da aka yi.
- Umarni a kan dogaro ga Allah, da tawakkali gareshi ba da waninsa ba, madalla da Shi a matsayin wakili.
- Imani da hukunci da ƙaddara da yarda da shi, kuma Allah Ya ƙaddara kowane abu.
- Wanda ya tozarta umarnin Allah, to, Allah Zai tozartashi ba zai kiyayeshi ba.