- Ruwa yana zama mai najasa idan ɗayan siffofinsa uku ya canza da najasa, launinsa, ko ɗanɗanonsa, ko warinsa, hadisin ya fita mafitar mafi rinjaye, ba wai akan iyakancewa ba.
- Malamai sun yi ijma'ai akan cewa ruwa idan najasa ta canja shi to ya zama mai najasa kai tsaye, daidai ne ya kasance kaɗan ne ko mai yawa.