- Ibadu an gina su ne akan abinda ya zone kawai a cikin Alkur’ani da sunna, ba zamu bautawa Allah - Madaukakin sarki - ba sai da abinda Ya shara'anta ba da bidi'o'i ko kirkirarrun abubuwa ba.
- Addini ba ra'ayi ba ne, ko ganin kyan abu, kadai da bin Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Wannan hadisin dalili ne akan cikar Addini.
- Bidi'a ita ce dukkanin abinda aka farar a Addini wanda babu shi a lokacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, da sahabbansa na akida ne ko magana ko aiki.
- Wannan hadisin tushe ne daga tushen Musulunci, shi kamar ma'auni ne ga ayyuka, kamar yadda kowanne aikin da ba'a nufi zatin Allah - madaukakin sarki - da shi ba, to mai aikata shi ba shi da wani lada, hakanan kowanne aikin da bai zama ya dace da abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi ba to shi abin juyarwa ne akan mai aikata shi.
- Fararrun abubuwan da aka hana su ne abinda suka kasance na al'amuran Addini, ba na duniya ba.