- Falalar Tauhidi da cewa wanda ya mutu yana mumini ba ya taranya Allah da wani abu zai shiga Aljanna.
- Hadarin shirka, cewa wanda ya mutu yana taranya Allah da wani abu zai shiga wuta.
- Masu Tauhidi wadanda suke sabo suna karkashin ganin damar Allah, in Ya so Ya azabtar da su, idan ya so Ya gafarta musu, sannan makomarsu tana ga Aljanna.