- Ma'anar shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi ne kadaita Allah da bauta, da barin bautar abinda ba shi ba.
- Ma'anar shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne shi ne imani da shi da kuma abinda ya zo da shi da gasgata shi, kuma cewa shi ne karshen Manzannin Allah zuwa ga dan Adam..
- Lallai cewa magana da mai ilimi da wanda yake tare da wata shubuha ba ta zama kamar magana da jahili ba; saboda haka ya fadakar da Mu'azu da fadinsa: "Lallai cewa kai zaka zo wa wasu mutane ma'abota littafi".
- Muhimmancin musulmi ya zama akan basira ga addininsa; dan ya kubuta daga shubuhohin masu sa shubuha, wannan ta hanyar neman ilimi kenan.
- Bacin addinin Yahudawa da Nasara bayan aiko Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma cewa su ba su zama daga masu tsira ba a ranar Kiyama har sai sun shiga addinin Allah, kuma sun yi imani da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.