- Kwaɗaitarwa a kan ikhlasi, domin cewa Allah ba Ya karɓar aiki sai abin da aka nufi zatinsa da shi.
- Ayyukan da ake neman kusancin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da su idan mukallafi ya aikata su a kan tafarkin al'ada, to, ba shi da wani lada a kansu, har sai ya yi nufin neman kusancin Allah da su.