- Tabbatar da ceto ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a lahira, kuma cewa shi ceton ba ya kasancewa sai ga masu Tauhidi.
- Cetonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne tawassalinsa zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - ga wanda ya cancanci shiga wuta daga masu Tauhidi cewa ba zai shigeta ba, wanda kuma ya shiga wutar da cewa zai fita daga cikinta muddin yana da Tauhidi.
- Falalar kalmar Tauhidi tsarkakkiyya ga Allah - Madaukakin sarki - da kuma girman tasirinta.
- Tabbatar da kalmar Tauhidi yana kasancewa ne da sanin ma'anarta, da kuma aiki da abinda taka kunsa.
- Falalar Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - da kuma kwadayinsa akan ilimi.