Bayani
Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a surar wani mutum namiji ba a sanshi ba, daga siffofinsa cewa tufafinsa masu tsananin fari ne, gashin kansa kuma mai tsananin baƙi ne, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi na bayyanar gajiya, da ƙura, da rarrabewar gashi, da dattin tufafi, kuma wani ɗaya daga mahalartan bai sanshi ba, alhali su suna zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai neman sani, sai ya tambayeshi game da musulunci, sai ya ba shi amsa da waɗannan rukunan, waɗanda suka ƙunshi iƙirari da shaida biyu, da kiyayewa a kan salloli biyar, da ba da zakka ga waɗanda suka cancanta, da azimin watan Ramadan, da ba da farillar Hajji a kan mai iko.
Sai mai tambayar ya ce: Ka yi gaskiya, sai sahabbai suka yi mamaki daga tambayarsa mai nuni a kan rashin saninsa a cikin abin da yake bayyana da kuma gasgatashi.
Sannan ya tambayeshi game da imani, sai ya amsa masa da waɗannan rukunan guda shida masu ƙunshe da imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da siffofinsa, da kaɗaitashi da ayyukansa kamar halitta, da kaɗaitashi da ibada, kuma cewa mala'iku waɗanda Allah Ya haliccesu daga haske bayi ne ababen girmamawa ba sa saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma suna aiki da umarninsa, da yin imani da littattafan da aka saukar ga manzanni daga Allah - maɗaukakin sarki -, kamar Al-ƙur'ani da At-Taura da Injila da wasunsu, da kuma (imani) da manzanni masu isar da Addinin Allah, daga cikinsu akwai Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da na ƙarshensu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -, da wasunsu daga Annabawa da manzanni, da imani da ranar lahira, abin da ke bayan mutuwa yana shiga cikinsu na kabari da rayuwar barzahu, kuma cewa mutum za a tasheshi bayan mutuwa kuma za a yi masa hisabi, kuma makomarsa za ta zama ko dai zuwa aljanna ko zuwa wuta, da imani da cewa Allah Ya ƙaddara abubuwa gwargwadon yadda iliminsa ya rigaya da shi, kuma hikimarsa ta hukuntashi da rubutunsa ga hakan, da mashi'arsa gareshi, da afkuwarsu gwargwadon yadda ya ƙaddarasu, ya kuma haliccesu don haka. Sannan ya tambayeshi game da kyautatawa, sai ya ba shi labari da cewa kyautatawa ita ce ya bautawa Allah kamar shi yana ganinsa, idan bai samu damar kaiwa zuwa wannan matsayin ba, to, ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - kamar Allah Yana ganinisa, na farko shi ne matsayin Mushahada, ita ce mafi ɗaukaka, na biyu shi ne matsayin Muraƙabah.
Sannan ya tambayeshi yaushe ne al-ƙiyama? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa, babu wani daga halitta da ya sanshi, wanda ake tambayar da mai tambayar.
Sannan ya tambayeshi game da alamomin al-ƙiyama? Sai ya bayyana masa cewa daga alamominta akwai yawan kuyangi (sa-ɗaka) da 'ya'yansu, ko yawan saɓawar 'ya'ya ga iyayensu, mata za su dinga yi musu mu'amala irirn mu'amalar bayi, kuma cewa makiyaya dabbobi da talakawa za a shinfiɗa musu duniya a ƙarshen zamani, sai su dinga alfahari a ƙawata gine-gine da ɗaukakasu.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari da cewa mai tambayar shi ne Jibrilu ya zo don sanar da sahabbai wannan addinin miƙaƙƙe.