- Bayanin hakkin Allah - madaukakin sarki - wanda ya wajabta shi akan bayinSa, shi ne su bauta maSa, kada su hada da komai.
- Bayanin hakkin bayi ga Allah - madaukakin sarki - wanda Ya wajabtaShi akan kanSa dan falala daga gareShi da kuma ni'ima, shi ne Ya shigar da su Aljanna, kada ya azabtar da su.
- A cikinsa akwai albishir mai girma ga masu kadaita Allah wadanda ba sa taranya wani abu daShi da cewa makomarsu (ita ce) shiga Aljanna.
- Mu'azu ya karantar da wannan Hadisin kafin mutuwarsa; dan tsoron fadawa a cikin zunubin boye ilimi.
- Fadakarwa akan rashin yada sashin Hadisai ga wasu mutane dan tsoron kada wanda bai riski ma'anarsuba; wannan a cikin abinda a karkashinsa babu wani aiki, kuma babu wani haddi daga haddodin Shari’a..
- Masu kadaita Allah masu sabo suna karkashin ganin damar Allah, in Yaso ya yi musu azaba, idan kuma Yaso Ya gafarta musu, sannan makomarsu tana ga Aljanna.