- Furta: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, da kuma ƙin yarda da duk abin da ake bautawa da ba Allah ba, sharaɗi ne na shiga Musulunci.
- Ma’anar (Babu abin bautawa da cancanta sai Allah), shi ne kafircewa duk abin da ake bautawa da ba Allah ba, na gumaka da ƙaburbura da sauransu, da kuma kaɗaita Allah da bauta.
- Wanda ya zo da Tauhidi, kuma ya lizimci dokokin Musulunci, to, wannan ya wajaba a kame daga gare shi, har sai wani abu da ya saɓawa hakan ya bayyana.
- Alfarmar dukiyar Musulmi da jininsa da mutuncinsa sai da haƙƙi [na shari'a].
- Hukunci a nan duniya a kan zahiri ne, a lahira kuma a kan niyya ne da manufofi.