- Kwaɗaitarwa akan haddace sunnar Annabi, da isar da ita ga mutane.
- Bayanin falalar ma'abota hadisi, da ɗaukakar nemansa.
- Falalar malamai waɗanda sune ma'abota istinbaɗi da fahimta.
- Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su -, su ne waɗanda suka ji hadisin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma suka isar da shi garemu.
- AlManawi ya ce: Ya bayyana anan cewa maruwaicin hadisi Fiƙihu ba sharaɗinsa ba ne, sharaɗinsa kawai shi ne hadda, kuma ya wajaba ga masanin fiƙihu fahimta da jujjuya ma'ana.
- Ibnu Uyaina ya ce: Babu wani da zai nemi hadisi sai a fuskarsa akwai ni'ima ga wannan hadisin.
- Hadda a wajen malaman hadisi nau'i biyu ce: Hadda ta zuciya da ƙirji, da hadda ta rubutu da zanawa, su biyun addu'ar a cikin hadisin ta ƙunshe su.
- Fahimace-fahimcen mutane mabanbanta ne, wataƙila wanda aka isarwa ya zama ya fi kiyayewa daga wanda ya ji, da yawa wanda ya dakko fiƙihu ya zama ba faƙihi ba.