- Tsaki iri biyu ne; Tsarki na zahiri, yana kasancewa ne da yin alwala da wanka, da kuma tsarkin badini yana kasancewa ne da kadaita Allah da imani da aiki na gari.
- Muhimmanicin kiyaye sallah, ita ce haske ga bawa a duniya da kuma ranar alkiyama.
- Sadaka dalili ce akan gaskiyar imani.
- Muhimmancin aiki da Alkur’ani da gasgata shi, dan ya zama hujja a gareka ba akanka ba.
- Rai idan ba ka shagaltar da ita da da'a ba, za ta shagaltar da kai da sabo.
- Kowanne mutum ba makawa sai ya yi aiki; kodai ya 'yanto ransa da biyayya (ga Allah) ko ya halakar da ita da sabo.
- Hakuri yana bukatar juriya da neman lada, kuma acikinsa akwai wahala.