/ Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa

Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa

Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.

Hadeeth benefits

  1. An so wannan adddu'ar a yayin shiga masallaci da fita daga cikinsa.
  2. Keɓance ambaton rahama a shiga, da falala a fita: saboda mai shiga ya shagalta da abin da zai kusanto da shi zuwa ga Allah da kuma aljannarSa, sai ya dace da ya ambaci rahama, idan ya fita zai tafi a ban ƙasa don neman falalar Allah da arziki, sai ya dace da ambaton falala.
  3. Waɗannan zikiran ana faɗinsu ne yayin nufin shiga masallaci, da yayin nufin fita daga cikinsa.