- Neman tsari ibada ne, kuma shi ne abin da ya kasance daga Allah maɗaukaki ko sunayanSa ko kuma siffofinSa.
- Halaccin neman tsarin Allah da zancenSa, domin sifa ce daga cikin siffofinSa mai tsarki, saɓanin neman tsari daga wani abin halitta wannan shirka ne.
- Falalar wannan Addu’ar da kuma albarkarta.
- Neman mafaka da zikiri dalili ne na tsare bawa daga sharri.
- Lalata neman tsari da wanin Allah kamar aljan da matsafa da shedanu da sauransu.
- Shar’antuwar wannan Addu’ar ga duk wanda ya sauka wani wuri a halin zaman gida ko tafiya.