- Girman yadda Musulunci ya kula da tsaftace kyawawan ɗabi’u da kuma cika su.
- Falalar kyawawan ɗabi’u, har suna kai bawa ya samu matsayin mai azumi wanda ba ya hutawa, mai nafilar dare wanda ba ya gajiya.
- Azumi da rana da Nafila da daddare ayyuka ne masu girma, suna da wahala ga rai, amma mai kyawawan ɗabi’u ya kai matsayinsu saboda ƙoƙari da ya yi a kansa da kyakkyawar mu’amala.