- Ya wajaba ga mumini ya yi nesa da mummunar magana da kuma mummunan aiki.
- Cikar ɗabi’un Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba abin da yake zuwa daga gare shi sai kyakkyawan aiki da daddaɗan zance.
- Kyawawan ɗabi’u wani fage ne da ake rige - rige, duk wanda ya Riga, ya kasance zababbe cikin muminai kuma mafi cikar imaninsu.