Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba
Daga Usama Ɗan Zaid Allah Ya yarda da su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin bai bar jarabawa a bayansa ba mafi cutar da Maza kamar mata ba, idan mace ta kasance cikin iyalansa ne, to, zai dinga kula da ita domin kada ta kaucewa Shari’a, idan kuma wata ce da ban, to, sabo da cuɗanya da kaɗaituwa da ita, da kuma irin barnar da zata biyo bayan haka.
Hadeeth benefits
Ya wajaba a kan Musulmi ya kiyayi fitinar mata, ya toshe duk wata hanya da za ta kai ga hakan.
Ya kamata ga Muminai riƙo da Allah da kwaɗayi a wurin sa domin kiyayewa daga fitintinu.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others