- Neman haƙƙin wanda aka zalunta da gaskiya ta hanyar kai ƙara, ba ya shiga cikin babin husumomi ababen zargi.
- Jayayya da husuma suna daga illolin harshe waɗanda suke sabbaba rabuwa da juya baya a tsakaknin musulmai.
- Jayayya abar yabo ce, idan ta kasance a kan gaskiya ne kuma usulubinta mai kyau, kuma tana kasancewa abar zargi idan ta kasance don dawo da gaskiya ne da tabbatar da ɓarna, ko ta kasance ba tare da hujja ba ko dalili.