- Hadisin dalili ne a kan haramcin zagin matattu.
- Barin zagin matattu a cikinsa akwai kula da maslahar rayayyu, da kiyaye zaman lafiyar jama'a daga gaba da ƙiyayya.
- Hikima a kan hana zaginsu, cewa sun isa zuwa abin da suka gabatar, to, zaginsu ba ya amfanarwa, kuma a cikinsa akwai cutarwa ga makusantansa rayayyu.
- Cewa ba ya kamata ga mutum ya faɗi abin da babu maslaha a cikinsa.