- Gargaɗi mai tsanani game da yaƙar musulmi ga 'yan uwansa musulmai.
- Daga mafi girman laifuka da ɓarna mai girma a ban ƙasa ɗaga makami a kan musulmai, da kuma ɓarna ta hanyar kisa.
- Narkon da aka ambata ba ya shafar yaƙin (da aka yi) da haƙƙi, kamar yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata da wasunsu.
- Haramcin tsoratar da musulmai da makami ko waninsa - ko da ta fuskar wasa ne ne -.