- Cancantar ukuba a kan wanda ya yi ƙudiri a kan saɓo da zuciyarsa, kuma ya aikata sabubbansa.
- Gargaɗi mai tsanani daga rigima tsakanin musulmai, da narko na wuta mai tsanani a kansa.
- Yaƙi tsakanin musulmai da gaskiya ba ya shiga cikin narkon, misalin yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata.
- Mai aikata babban laifi ba ya kafirta saboda aikata saɓon; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ambaci masu yakin (da) musulmai.
- Idan musulmai suka haɗu ta kowace sila ce a ka yi yaƙi a cikinta, sai ɗayansu ya kashe ɗayan, to, wanda ya yi kisan da wanda a ka kashe suna cikin wuta, ambaton takobi a cikin hadisin ta hanyar misaltawa ne.