- Hani game da ramuwa da sama da abin da aka yi.
- Allah bai umarci bayainsa da wani abu da zai cutar da su ba.
- Haramta cuta da cutarwa ta magana ko da aiki ko da bari.
- Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki, wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cuta, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawa.
- Daga ƙa'idojin shari'a akwai: "Cuta ana gusar da ita", shari'a ba ta tabbatar da cuta, kuma tana inkarin cutarwa.