- Falalar adalci da kwaɗaitarwa a kansa.
- Adalci mai gamewa ne ya tattaro dukkanin shugabanci da hukunci a tsakanin mutane, har adalci a tsakanin ma'aurata da 'ya'ya da sauransu.
- Bayanin matsayin masu adalci a ranar al-ƙiyama.
- Banbance-banbancen matsayiyyikan ma'abota imani a ranar al-ƙiyama kowanne da gwargwadon aikinsa.
- Salon kwaɗaitarwa yana daga salon kiran da zai kwaɗaitar da wanda ake kira a aikin ɗa'a.