- Bayanin sashin almomin munafuki dan tsoratarwa da gargaɗarwa daga afkawa a cikinsu.
- Abin nufi daga Hadisin: Cewa waɗannan ɗabi'un sune ɗabi'un munafunci, kuma mai su mai kama da muanfukai ne a cikin waɗannan ɗabi'un, kuma mai ɗabi'antuwa ne da ɗabi'unsu, ba dan cewa shi munafuki ne mai bayyanar da musulunci ya ɓoye kafirci ba, an ce wannan abin ɗauka ne ga wanda waɗannan ɗabi'un suka rinjaye shi kuma ya yi sakaci da su, ya wulaƙantar da al'amarinsu; wanda ya zama kamar hakan to ya zama mai ɓatacciyar aƙida a galibi.
- AlGazali ya ce: Asalin addini mai taƙaituwa ne a cikin abubuwa uku: Faɗa, da aikatawa, da niyya.
- Sai ya faɗakar akan ɓacin magana da ƙarya, da kuma ɓacin aiki da ha'inci, da kuma ɓacin niyya da saɓawa alkawari; domin cewa saɓa alƙawari ba ya kawo cikas sai dai idan ƙudirin niyyar akansa ya kasance mai gwamuwa da alƙawari, amma da ya kasance mai ƙudirin niyya da gaske sai wani abu mai hanawa ya bijiro masa ko wani ra'ayi ya bayyana gare shi to wannan ba'a samu surar munafunci daga gare shi ba.
- Munafunci nau'i biyu ne: Munafunci na aƙida yana fitar da mai shi daga imani, shi ne bayyanar da Musulunci da ɓoye kafirci. Da munafunci na aiki, shi ne kamanceceniya da munafukai a cikin ɗabi'unsu, wannan ba ya fitar da mai shi daga imani, sai dai cewa shi babban laifi ne daga manyan laifuka.
- Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa malamai sun haɗu akan cewa wanda ya zama mai gaskiya da zuciyarsa da harshansa kuma ya aikata waɗannan ɗabi'un ba'a yi masa hukunci da kafirci, kuma shi ba munafukin da za'a dawwamar a cikin wuta bane.
- AlNawawi ya ce: Wasu jama'a daga malamai sun ce: Abin nufi munafukan da sun kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka zantar da imaninsu, kuma suka yi ƙarya, kuma aka amince musu akan addininsu sai suka yi ha'inci, kuma suka yi alƙawari a cikin al'amarin addini suka taimake shi sai suka saɓa, kuma suka fajircewa abokanan husumarsu.