- Abin da zai hana ka alheri ba a ambatonsa kunya, kai ana ambatonsa tsoro da gajiyawa da rauni da ragonta.
- Kunyar Allah - Mai girma da daukaka - tana kasancewa ne da aikata abubuwan da aka umarta, da barin abubuwan da aka hana.
- Kunyar ababen halitta tana kasancewa ne da girmamasu, da saukar da su masaukansu, da nisantar abin da zai munana a al'adance.