- Falalar haƙuri da kiyaye rai a lokacin fushi, kuma cewa yana daga cikin ayyuka na gari waɗanda musulunci ya kwaɗaitar a kansu.
- Yaƙar zuciya a lokacin fushi shi ne mafi tsanani daga yaƙar maƙiyi.
- Canjawar musulunci ga fahimtar ƙarfi irin na Jahiliyya zuwa ɗabi'u masu girma, to, mafi tsananin mutane a karfi shi ne wanda ya mallaki ragamar kansa.
- Nisanta daga fushi; saboda abin da yake jawowa na cutarwa a kan ɗaiɗaiku da jama'a.