- Kore imani a cikin nassosin shari'a ba ya kasancewa sai dan aikata wani aiki na haramun ko barin wajibi.
- Kwaɗaitarwa akan kiyaye gaɓɓai da kiyayesu daga munanan abubuwa, musamman ma harshe.
- Assindi ya ce: A cikin sigar mubalaga a cikin (mai yawan suka, da mai yawan tsinuwa) akwai nuni akan cewa idan suka da tsinuwa sun zama kadan ne ga wanda yake cancantar hakan ba ya cutarwa a cikin siffantuwa da siffofin ma'abota imani.