- Kiyayewa akan waɗannan kalmomin dan koyi da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Mutum kamar yadda shi abin umarta ne da roƙon Allah lafiya a cikin Addini kamar haka shi abin umarta ne da roƙonta a duniya.
- Al-Ɗaibi ya ce: Ya game ɓangarori shida ne; domin cewa aibuka daga garesu ne, kuma yakai matuƙa a ɓangaren ƙasa dan munin aibukan daga gareta ne.
- Abin da yafi a karanta zikirai, a safiya: Daga ɓollowar alfijir zuwa ɓullowar rana a farkon yini, haka kuma daga bayan la'asar zuwa kafin faɗuwar rana, idan ya faɗesu bayan hakan yana nufin: Ya faɗesu a safiya bayan ɗagawar walaha ya isar masa, idan ya faɗesu bayan azahar ya isar masa, idan ya faɗesu bayan Magariba ya isar masa, to wannan lokaci ne na zikiri.
- Dalili bai yi nuni ba akan kasancewar zikiri yana da lokaci ayyananne ba a cikin dare kamar karanta ƙarshen ayoyi biyu daga Suratul Baƙarah cewa ita tana kasancewa ne da daddare bayan faɗuwar rana.