- Fifikon 'yan aljanna a matsayinsu, hakan kuma gwargwadan imani da ayyuka na gari.
- Kwaɗaitarwa akan roƙon Allah Firdausi maɗaukakiya daga gidajan aljanna.
- Firdausi ita ce mafi ɗaukakar gidajan aljanna, kuma mafificinsu.
- Yana kamata ga musulmi himmarsa ta zama maɗaukakiya, kuma ya yi ƙoƙari ya nemi mafi ɗaukakar matsayai kuma mafifitansu a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Ƙoramun aljanna huɗu su ne ƙoramun ruwa da nono da giya da zuma waɗanda aka ambata a ciki AlƘur'ani a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -; {Kwatankwacin aljannar da aka yi wa masu tsoron Allah alƙawari a cikinta akwai ƙoramu na ruwa ba mai sakewa ba, da ƙoramu na nonon da ɗanɗanonsa bai canja ba, da ƙoramu na giya masu ɗaɗi ga masu sha da ƙoramai na tatacciyar zuma} [Muhammad: 15].