- Ba a sharɗanta tsarkin ƙaramin hadasi ko babba a ambaton Allah ba.
- Dawwamar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ambaton Allah maɗaukaki.
- Kwaɗaitarwa a kan yawaita ambaton Allah maɗaukaki a kowanne lokaci domin koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a yanayin da aka hana ambaton Allah kamar lokacin biyan buƙata.