Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku".
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa imani yana tsufa a cikin zuciyar musulmi kuma yana rauni kamar sabon tufafin da yake tsufa saboda tsawon amfani da shi. Saboda yankewa a ibada, ko aikata sabo da afkawa a cikin sha'awowi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da cewa mu roki Allah - Madaukakin sarki - ya sabunta imaninmu, ta hanayar tsayuwa da wajibai da yawan zikiri da istigfari.
Hadeeth benefits
Kwadaitarwa akan rokon Allah tabbata da sabunta imani a cikin zuciya.
Imani fada ne da aikatawa da kudircewa, yana karuwa da biyayya, kuma yana raguwa da sabo.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others