- Koyarwar mutum ga iyalansa abinda zai anfanar da su daga al'amuran Addini da duniya, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga (Nana) A'isha.
- Abinda ya fi ga musulmi ya haddace addu'o'in da suka zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa su suna daga addu'o'i dunkulallu.
- Malamai sun faɗa game da wannan hadisin: Shi ne mafi tattarowar hadisai a roƙon alheri da neman tsari daga sharri, shi yana daga kalmomi masu tattarowa (kalmomi kaɗan masu ɗaukar ma'anoni masu yawa) waɗanda aka bawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - su.
- Daga sabubban shiga aljanna bayan rahamar Allah: Ayyuka da kalamai na gari.