- Imani yana da zaƙi da ɗanɗano da yake zaƙaƙa zukata, kamar yadda zaƙin abinci da abin sha suke zaƙaƙa baki.
- Jiki ba ya samun zaƙin abinci da abin sha sai a lokacin lafiyarsa, to haka nan zuciya idan ta kuɓuta daga cututtukan soye-soyen zuciya masu ɓatarwa da sha'awowi ababen haramtawa, to ya samu zaƙin imani, a duk lokacin da ya samu rashin lafiya da masassara ba zai samu zaƙin imani ba, kai zai iya jin zaƙin abinda a cikinsa akwai halakarsa da son zuciya da saɓo.
- Mutum idan ya yarda da wani al'amari kuma ya so shi to al'amarinsa zai yi sauƙi gare shi, wani abu daga gare shi ba zai yi masa wahala ba, kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi, kuma zuciyarsa ta cakuɗa da walwalarsa, to haka nan mumini idan imani ya shiga zuciyarsa, to sai biyayyar Ubangijinsa ta sauƙaƙa gareshi kuma ransa ya ji daɗi gareta, wahalhalunta ba zasu wahalar da shi ba.
- Ibunl-Kayim ya ce: Wannan Hadisin ya ƙunshi yarda da RububiyyarSa - tsarki ya tabbatar maSa da UluhiyyarSa, da yarda da ManzonSa da jawuwa gareShi, da yarda da addininSa da miƙa wuya gare shi.