- Halaccin baiwa mutum labari da sonsa a lamarin Allah.
- An so yin wannan addu'ar a bayan kowace sallar farilla da nafila.
- A cikin yin addu'a da waɗannan lafuzan 'yan kaɗan (akwai) abbuwan nema a duniya da lahira.
- Daga fa'idojin soyayya a lamarin Allah yin wasicci da gaskiya da yi wa juna nasiha da taimakekeniya akan aikin alheri da tsoron Allah.
- Malam al-Ɗaibi ya ce: Ambatan Allah shi ne kan gaba a buɗewar ƙirji, godiyarSa kuma tsani ce na ni'imomi ababen amsawa, kyakkyawar ibada kuwa abar nema daga gare shi, shi ne nisantar abinda zai shagaltar da shi daga Allah - Maɗaukakin sarki -.