- Bayanin falalar Allah ga bayinSa muminai da kuma rahamarSa garesu ta hanyar gafarta zunubai da mafi karancin cutar da zata samesu.
- Ya kamata ga musulmi ya nemi ladan abinda ya sameshi a wurin Allah, ya kuma yi hakuri akan dukkanin karami da babba, dan ya zama yana samun daukakar darajoji da kuma kankarewa ga munanan laifuka.