- Bayanin shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a atishawa, da kuma koyi da shi a hakan.
- An so (mai atishawa ya) ɗora tufafi ko hankici da makancinsa akan bakinsa da hancinsa idan zai yi atishawa, domin kada wani abinda zai cutar da abokin zamansa ya fito daga gare shi.
- Kanƙar da murya a atishawa abin so ne, hakan yana daga cikar ladabi, da kuma kyawawan ɗabi'u.