- Falalar godiya akan farin ciki da kuma haƙuri akan cuta, wanda ya aikata hakan alherin duniya da na lahira za su same shi, wanda bai godewa ni'ima ba, kuma bai yi haƙuri akan musiba ba, to lada ya wuce shi, kuma zai samu zunubi.
- Falalar imani, kuma cewa lada a kowanne hali ba ya kasancewa sai ga ma'abota imani.
- Godiya a lokacin farin ciki, da haƙuri akan cuta suna daga ɗabi'un mumini.
- Imani da hukuncin Allah da kuma ƙaddararSa yana sanya mumini a cikin cikakkiyar yarda a kowanne halinsa, saɓanin wanin mumini wanda yake kasancewa a cikin fushi, idan ya sami Ni’ima daga Allah madaukakin sarki sai ya shagalta da ita daga biyayya ga Allah, amadadin haka ma sai ya juyar da ita a saɓonSa.