- Hanin zuwa masallaci ga wanda ya ci tafarnuwa, ko albasa, ko algarif.
- Ana riskar da waɗannan abubuwan, dukkan abinda yake da warin da masallata suke cutuwa daga gare shi, kamar warin taba da wiwi da makancin hakan.
- Illar hanin “wari”, idan ya gushe da yawan dafuwa ko wanin hakan; to karhancin ya gushe.
- Karhancin cin waɗannan abubuwan ga wanda zuwa sallah a masallaci ya wajaba akansa; dan kada jam'i ya wuce shi a cikin masallaci, muddin dai bai ci ba dan dabara akan kin halarta, to (cin) ya haramta.
- Hanuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga cin tafarnuwa da makancinsa, badan haramcinsa ba ne, kawai dan ganawarsa ne da (mala'ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -.
- Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da bayanin sababinsa; dan wanda ake magana ya nutsu da sanin hikimar.
- Alkali ya ce: Malamai sun ƙiyasta wanin masallaci akan wuraren haɗuwa dan yin sallah, kamar wurin sallar idi da jana'iza da makancinsu daga wuraren taruwa dan yin ibadu, haka nan wuraren taruwa na ilimi da zikiri da walimomi da makancinsu, ba za'a riskar da kasuwanni da wasunsu da su ba.
- Malamai sun ce: A cikin wannan hadisin akwai dalili akan hana cin tafarnuwa da makamancinta daga shiga masallaci - koda ya kasance ba kowa - domin shi guri ne na mala'iku, kuma saboda gamewar hadisan.