- Wajabcin riƙo da addini, da gaggawa a aiki na gari kafin abubuwan da zasu hana su hana.
- Nuni zuwa bibiyar fitinu masu ɓatarwa a ƙarshen zamani, kuma cewa duk lokacin da wata fitina ta tafi sai wata fitinar daban ta biyo bayanta.
- Idan addinin mutum ya yi rauni kuma ya sauka daga gare shi, saboda al'amuran duniya na dukiya ko waninta, to hakan zai zama sababi a karkacewarsa da barinsa ga addini da binsa tare da fitintinu.
- A cikin Hadisin akwai dalili akan cewa ayyuka na gari sababi ne na tsira daga fitintinu.
- Fitintinu sun rabu biyu: Fitintinu na shubuhohi, to kuma maganin su shi ne ilimi, da fitintinu na Sha’awa, to kuma maganin su shi ne imani da haƙuri.
- A cikin Hadisin akwai nuni zuwa cewa wanda aikinsa ya ƙaranta to fitina zata fi gaggawa zuwa gare shi, kuma wanda aikinsa ya yi yawa to yana kamata kada ya ruɗu da abinda ke tare da shi, kawai ya nemi ƙari.