- An so godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a ƙarshen cin abin ci.
- Bayanin girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, inda Ya azirtasu kuma Ya sawwaƙa musu sabubban arziƙi , kuma Ya sanya kankare munanan ayyuka a cikin hakan.
- Al'amuran bayi gabaɗayansu daga Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, ba da dabararsu ko ƙarfinsu ba, kuma bawa abin umarta ne da aikata sabubba.