- Daga cikin rahamar Allah ga bayinSa muminai shi ne ya kankare musu zunubansu a duniyarsu ta hanyar wasu masibu na duniya da aibobinta.
- Bala'i shi akarankansa yana kankare zunubai da sharaɗin imani, idan bawa ya yi hakuri bai yi fushi ba za'a ba shi lada.
- Kwaɗaitarwa akan hakuri a dukkan al'amura, cikin abinda yake so da abinda yake ki, ya yi hakuri har ya bada abinda Allah Ya wajabta masa, kuma ya yi hakuri har ya nisanci abinda Allah Ya haramta, yana kwaɗayin ladan Allah, kuma yana tsoron ukubarSa.
- FaɗinSa: "Da mumini da mumina", karin lafazin mumina a cikinsa akwai dalili akan karin karfafawa ga mace; in ba haka ba da ya ce: "Da mumini" da mace ta shiga cikinsa; domin hakan ba ya kebantar namiji, idan bala'i ya afkawa mace to haka itama an yi mata alkawari da kwatankwacin wannan sakamakon na kankare zunubai da kurakurai.
- Falalar da ta jerantu akan bala'i tana daga abinda zai sawwakawa bawa abinda yake gamuwa da shi na raɗaɗi akai akai.