{Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.} (سورة المائدة
: 2).
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحِلُّواْ شَعَٰٓئِرَ ٱللَّهِ وَلَا ٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَلَا ٱلۡهَدۡيَ وَلَا ٱلۡقَلَٰٓئِدَ وَلَآ ءَآمِّينَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّهِمۡ وَرِضۡوَٰنٗاۚ وَإِذَا حَلَلۡتُمۡ فَٱصۡطَادُواْۚ وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُواْۘ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi.} (سورة المائدة
: 94).
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَيَبۡلُوَنَّكُمُ ٱللَّهُ بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلصَّيۡدِ تَنَالُهُۥٓ أَيۡدِيكُمۡ وَرِمَاحُكُمۡ لِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَخَافُهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ
{Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama*. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.} (سورة المائدة
: 95).
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡتُلُواْ ٱلصَّيۡدَ وَأَنتُمۡ حُرُمٞۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآءٞ مِّثۡلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحۡكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ هَدۡيَۢا بَٰلِغَ ٱلۡكَعۡبَةِ أَوۡ كَفَّٰرَةٞ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوۡ عَدۡلُ ذَٰلِكَ صِيَامٗا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمۡرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنۡ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنۡهُۚ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ
{An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku.} (سورة المائدة
: 96).
أُحِلَّ لَكُمۡ صَيۡدُ ٱلۡبَحۡرِ وَطَعَامُهُۥ مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِلسَّيَّارَةِۖ وَحُرِّمَ عَلَيۡكُمۡ صَيۡدُ ٱلۡبَرِّ مَا دُمۡتُمۡ حُرُمٗاۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
{Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani* ne.} (سورة المائدة
: 97).
۞ جَعَلَ ٱللَّهُ ٱلۡكَعۡبَةَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ قِيَٰمٗا لِّلنَّاسِ وَٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَٱلۡهَدۡيَ وَٱلۡقَلَٰٓئِدَۚ ذَٰلِكَ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ
{Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne Azzãlumai.} (سورة التوبة
: 19).
۞ أَجَعَلۡتُمۡ سِقَايَةَ ٱلۡحَآجِّ وَعِمَارَةَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ كَمَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَجَٰهَدَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ لَا يَسۡتَوُۥنَ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ
{"Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi."} (سورة الحج
: 27).
وَأَذِّن فِي ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَجِّ يَأۡتُوكَ رِجَالٗا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٖ يَأۡتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٖ
{"Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci."} (سورة الحج
: 28).
لِّيَشۡهَدُواْ مَنَٰفِعَ لَهُمۡ وَيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡلُومَٰتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۖ فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡبَآئِسَ ٱلۡفَقِيرَ
{"Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ¦ãkin nin 'yantacce."} (سورة الحج
: 29).
ثُمَّ لۡيَقۡضُواْ تَفَثَهُمۡ وَلۡيُوفُواْ نُذُورَهُمۡ وَلۡيَطَّوَّفُواْ بِٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ
{Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni* a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ¦ãkin 'yantacce ne.} (سورة الحج
: 33).
لَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ مَحِلُّهَآ إِلَى ٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ
{Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye* a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa.} (سورة الحج
: 36).
وَٱلۡبُدۡنَ جَعَلۡنَٰهَا لَكُم مِّن شَعَٰٓئِرِ ٱللَّهِ لَكُمۡ فِيهَا خَيۡرٞۖ فَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا صَوَآفَّۖ فَإِذَا وَجَبَتۡ جُنُوبُهَا فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡقَانِعَ وَٱلۡمُعۡتَرَّۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرۡنَٰهَا لَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
{Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi.} (سورة الحج
: 37).
لَن يَنَالَ ٱللَّهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَآؤُهَا وَلَٰكِن يَنَالُهُ ٱلتَّقۡوَىٰ مِنكُمۡۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمۡ لِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُحۡسِنِينَ