- Wajibcin son Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma gabatar da shi a kan son duk wani da a ka halitta.
- Daga cikin alamomin cikar so: Taimakawa Sunnar Ma’aikin Allah, da kuma bayar da rai da dukiya a kan haka.
- Son Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana hukunta yi masa biyayya a abin da ya yi umarni da kuma gasgata shi a abin da ya ba da labari da kuma nisantar abin da ya hana kuma ya tsawatar, da bin Sa, da kuma barin Bid’a.
- Haƙƙin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne mafi girma mafi ƙarfi a kan na kowa, domin ya kasance shi ne dalilin shiriyarmu daga ɓata da kuma tseratar da mu daga wuta, da rabauta da aljanna.