Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar sallah a masallacinsa, kuma cewa shi yafi yawan lada daga sallah dubu a cikin waninsa daga masallatan duniya, sai dai Masallaci mai alfarma a Makka, shi ne mafifici daga sallah a cikin masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Hadeeth benefits
Ruɓanya ladan sallah a cikin Masallaci mai alfarma, da masallacin Annabi.
Sallah a Masallaci mai alfarma ita ce mafi alheri daga sallah dubu a wasu masallatan da ba su ba.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others