Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki
Daga Imaran Ɗan Husain Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na kasance Ina da basir, sai na tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da sallah sai ya ce: Ka yi Sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba, to, a zaune, idan ba za ka iya ba, to, a ɓarin jiki.
Buhari ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana asali a Sallah shi ne a yi ta a tsaye, sai idan ba za a iya ba, sai a yi ta a zaune, idan ba zai iya sallar a zaune ba, to, ya samu ya yi a gefen jikinsa.
Hadeeth benefits
Sallah ba ta faɗuwa muddin hankali na nan, sai ya kasance daga wannan yanayin, zuwa wancan yanayin gwargwadon damar da yake da ita.
Sauƙi da rangwamen Musulunci cewa bawa zai aikata ibada yadda yake da iko.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others