- Haramta zance alokacin jin huɗuba, ko da da hani ne daga abin ƙi, ko amsa sallama da gaishe da mai atishawa.
- An togance wanda yake yi wa liman magana, ko liman yake yi masa magana [daga wannan hanin].
- Halaccin yin magana a lokacin huɗubobi biyu a yayin buƙata.
- Idan an ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali liman yana huɗuba, to, za ka yi masa salati, a ɓoye, haka nan cewa amin ga addu'a.