- An so yin sallah raka'a biyu gaisuwa ga masallaci kafin zama.
- Wannan umarni ne ga wanda ya yi nufin zama, wanda ya shiga masallaci ya fita kafin ya zauna umarnin bai shafe shi ba.
- Idan mai sallah ya shiga (masallaci) alhali mutane suna cikin sallah, sai ya shiga cikinta tare da su, to, wannan ya wadatar masa daga raka'o'i biyun.