- An so sallah tsakanin kiran sallah da iƙama.
- Shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a maimaita magana, hakan dan jiyarwa da ƙarfafawa ga muhimmnacin abinda yake faɗa.
- Abin nufi da kiran sallah biyu: Kiran sallah da iƙama, kuma ya anbace su da (lafazin) (Kiran sallah biyu) dan rinjayarwa, kamar wata biyu (Rana da wata) da Umar biyu (Abubakar da Umar).
- Kiran sallah shi ne sanar da shigar lokaci, iƙama kuma ita ce sanar da halartar yin sallah.