Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba)
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).
Buhari ne ya rawaito shi
Bayani
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lazimta akan sallolin nafilfili a ɗakinta kuma ba ya barinsu: Raka'o'i huɗu da sallama biyu kafin sallar Azahar, da kuma raka'o'i biyu kafin sallar Asuba.
Hadeeth benefits
An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin sallar Azahar, da raka'a biyu kafin sallar Asuba.
Abinda ya fi shi ne ka sallaci (salloli) ratibai a cikin gida, da haka ne Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others